1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gabatar da sakamako kan harbe-harbe a Amirka

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 7, 2019

A Amirka masu bincike sun gabatar da sakamakon farko na harbe-harben da suka yi sanadiyyar mutane da dama a karshen mako a biranen El Paso da Dayton na jihohin Texas da Ohio.

https://p.dw.com/p/3NTod
USA Trauer nach der Schießerei in Dayton, Ohio
Hoto: picture-alliance/newscom/UPI/J. Sommers II

A kasar Amirka sakamakon farko na binciken da hukumar 'yan sanda ta soma kan 'yan bindiga dadin nan da suka buda wuta tare da halaka jama'a da dama a karshen makon da ya gabata a biranen El Paso na jihar Texas da kuma Dayton na jihar Ohio ya nunar da cewa dan bindigar na farko Patrick Crusius dan shekaru 21 wanda ya halaka mutane 22 tare da jikkata da dama a ranar Asabar a jihar Texas na da akidar kyamar bakin haure ne musamman 'yan asalin kasashen Latin Amirka. 

Masu binciken sun gano cewa sai da Crusius ya wallafa wani sharhi na kyamar bakin haure a saman intanet kafin ya je ya buda wuta kan jama'a a wani babban shago na birnin El Paso na jihar Texas wanda kaso 83 daga cikin dari na mazaunansa 'yan asalin kasashen Latin Amirka ne. 

Dan bindigar na biyu Connor Bretts dan shekaru 24 wanda ya halaka mutane tara da suka hada da kanwarsa a daren Lahadi a birnin Dayton na jihar Ohio kafin 'yan sanda su bindige shi, na da akidar kyamar mata. 

Bayan afkuwar wannan lamari, Shugaba Donald Trump ya yi kira ga Majalisar dokokin kasar ta Amirka da ta gudanar da gyaran huska ga dokar mallakar makami a kasar.