Amirka: Republican ta sha kaye a zabe | Labarai | DW | 08.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Republican ta sha kaye a zabe

A kasar Amirka jam'iyyar Republican ta Shugaba Donald Trump ta sha kaye a zaben kananan hukumomi a jihohin kasar da dama da suka hada da Virginia da New Jersey.

'Yan takarar neman kujerar gwamna daga jam'iyyar Democrats ne suka yi nasarar doke abokanan hamayyarsu na jam'iyyar Republican masu kusanci da Shugaba Trump. Ralph Northam na jam'iyyar Democrates shi ne sabon zabebben gwamnan na jihar Virginia ya kuma ce "al'umma ta bukaci da mu kawo karshen rarrabuwar kawunan da ta fuskanta a sakamakon siyasar kyama da wasu suka yada. To ina mai tabbatar maku da cewa ga likitan da zai warkar da wannan cuta daga yanzu" 

Wannan zaben kananan hukumomi ya kasance tamkar na raba gardama kan matsayin Amirkawa a kan mulkin Shugaba Donald Trump wanda a wannan Laraba ya ke bikin cikar shekara daya da lashe zaben shugaban kasar ta Amirka.  A birnin New York ma dai dan takarar jam'iyyar adawa ta Democrates Bill de Blasio ne ya lashe zaben da gagarimin rinjaye na kashi 65 daga cikin dari na kuri'un da aka kada.