Tsamin diflomasiyya tsakanin Amirka da Chaina
February 4, 2023Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta sake hango karin na'urar da ta kira ta leken asirin Chaina a karo na biyu, tana mai cewa an ga kumbon na shawagi a sararin samaniyar kasar.
Hukumomin tsaron kasar ba su yi wani karin haske kan inda suka tantace na'urar ba, da suke zargin Chaina na amfani da ita ne wajen tatso wasu bayanan sirri.
Tuni hukumomin Sin, suka ci gaba da nacewa kan na'urorin na har-hada wasu bayanan kimiyya ne kawai. Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta nuna rashin ji dadin yadda na'urar farkon ta karkace daga jadawalin da aka shata mata ba.
Wannan lamarin dai ya haifar da 'yar tsamar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, wanda har ta kai ga babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken jingine ziyarar kwanaki biyu da zai kai a Chaina.