1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Amirka: Johannesburg na iya fuskantar hari

Mouhamadou Awal Balarabe
October 26, 2022

Ofishin jakadancin Amirka a Afirka ta Kudu ya yi gargadin cewa birnin Johannesburg na cikin hatsarin fuskantar harin ta'addanci nan ba da jumawa ba. Amma bai bayyana dalili ba.

https://p.dw.com/p/4Iiwi
Rukunin sabbin gidajen da aka gina a Afirka ta KuduHoto: Shafiek Tassiem/Reuters

Amirka ta gargadi Afirka ta Kudu game da hadarin fuskantar hari a ranar Asabar kan "manyan taruka" da za a gudanar a arewacin Johannesburg babban birnin kasar. Sai dai cikin sanarwa da ofishin jakandanci Amirka ta watsa a shafinta na intanet, ba ta yi karin bayani game da lokaci da hanya da za a bi da kuma manufar wannan harin ba.

Amma ma'aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu ta ki ta ce uffan game da wannan barazana a lokacin da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntubi wasu jami'an gwamnati. Babu dai wani hari da aka kai wa Afirka ta Kudu a shekarun baya-bayan nan. Sai dai ta zama kasa ta biyu da Amirka ta shawarta da takaita zirga-zirgar jama'a saboda yiwuwar hare-haren ta'addanci, baya ga tarayyar Najeriya.

Fiye da sojojin Afirka ta Kudu dubu daya ne ke taimaka wa a makwabciyar kasar Mozambik domin karya lagon masu ikirarin jihadi da ke dauke da makamai.