1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya lashe zaben jihohin Texas da Massachusetts

Abdourahamane Hassane
March 4, 2020

Joe Biden tsohon mataimakin shugaban kasa na Amirka ya lashe zaben fitar da gwani na dan takarar jam'iyyar Democrats a Texas da Massachusetts da wasu jhohin wanda ya ce suna kan hanyar samun sauyin mulki.

https://p.dw.com/p/3YpnX
USA Super Tuesday | Joe Biden in Los Angeles
Hoto: Getty Images/AFP/M. Tama

A sama da jihohi goma na zaben share-fage na jam'iyyar hamayya ta Demokrats, tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden ya samu nasara,  inda a Texas ya doke Bernie Sanders da kuma Elizabeth Warren a Jihar Massachusetts. A shirye-shiryen fitar da gwanin dan takarar da zai fafata da Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican mai mulki a zaben watan Nuwambar bana. Joe Biden ya ce wannan wata alama ce ta kawo karshen mulkin Donald Trump a Amirka.