1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin shugaba Joe Biden ga 'yan majalisu

Binta Aliyu Zurmi
February 8, 2023

Shugaban Joe Biden na Amirka a babban jawabinsa na shekara ga 'yan majalisun kasar ya yi kira a garesu da su bashi hadin kai da zai bashi damar kammala ayyukan ci gaban al'umma da ya fara.

https://p.dw.com/p/4NDY8
USA Washington | State of the Union | Joe Biden
Hoto: Saul Loeb/AFP

A jawabinsa na mintuna 73 a zaman hadin gwiwa na majalisun kasar, Shugaba Biden ya bayyana irin nasororin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru biyu musanman a fannin ilimi da kiwon lafiya da kyautatawa iyali da kuma habakar tattalin arziki 

Shugaban na Amirka ya kuma bayyana rashin jin dadinsa ga wasu matsalolin da kasar ke fuskanta musanman masu nasaba hare-haren 'yan bindiga da aikata manyan laihuka da kuma yadda dangantaka takan yi tsami a tsakanin ‘yan sanda da al'umma.

Shugaba Biden ya kuma kalubalanci 'yan jam'iyyar adawa ta Republican da su tallafa dago da bshin da kasar ke da shi gami da goyon bayan manufofi da za su taimakawa masu karamin karfi a kasar.