1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da zanga-zanga a Amirka

Zulaiha Abubakar
May 31, 2020

Yayin da kasar Amirka ke fuskantar zanga-zangar kisan wani Bakar Fata, yanzu haka dai lauyan iyalan mamacin na duba yiwuwar shigar da sabuwar kara game da yadda 'Dan sanda ya danne marigayin har ransa ya fita.

https://p.dw.com/p/3d4tQ
USA Minneapolis Polizei |Tod eines Schwarzen Mannes
Hoto: AFP/Facebook/Darnella Frazier

Lauya Ben Crump ya kara da cewar yana da tabbacin za a samu shaidun da zasu tabbatar da cewar 'dan sandan Derek Chauvin mai shekaru 44 ya gudanar da wannan mummunar aika-aika ne da gangan.

Binciken da likitoci suka gudanar kan gawar George Floyd ya nunar da cewar daga cikin abubuwan da suka yi sanadiyyar mutuwarsa akwai shakar da 'Dan sandan ya yi masa da lalurar ciwon zuciya da ya ke fama da ita da kuma alamun barasa a jikinsa. Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye rubuce da kalmommin marigayi Floyd na karshe watau ''na kasa numfashi''.