Amirka: Hadarin jirgin kasa ya halaka mutane biyu | Labarai | DW | 04.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Hadarin jirgin kasa ya halaka mutane biyu

Mutane biyu sun mutu a yayin da wasu mutune fiye da 110 suka samu rauni a sanadiyar hadarin jirgin kasa da ya faru a Jihar Kudancin Carolina a kasar Amirka.

Gwamnan jihar Kudancin Carolina Henry Mcmaster ya ce ga dukkan alamu, jirgin ya saki hanyar da ya kamata ya bi kafin daga bisani ya ci karo da wani jirgin dakon kaya da ke tsaye. Ma'aikatan jirgin biyu ne suka mutu, an gano fasinjoji dari da talatin da tara da ma'aikata takwas ne a cikin jirgin a lokacin da aka yi hadarin, daya jirgin da aka yi karo da shi babu mutum ko daya a ciki inji gwamnan.

Masu aikin ceto sun kwashe duk fasinjojin daga cikin jirgin. Shugaba Donald Trump da ke bin diddigin labarin aukuwar hadarin, ya meka sakonsa na jaje ga iyalai dama sauran al'umma da al'amarin ya shafa.