1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyaran huska da dokar aikin 'yan sanda a Amirka

Gazali Abdou Tasawa
June 17, 2020

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi garanbawul da dokar tsarin aikin 'yan sanda a wani mataki na amsa kiran masu zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a Amirka musamman ta 'yan sanda kan bakar fata.

https://p.dw.com/p/3dtnz
USA Trump unterschreibt Ausführungsverordnung zur sicheren Polizeiarbeit
Hoto: picture-alliance/CNP/MediaPun/S. Reynolds

A sakamakon matsin lambar masu zanga-zangar adawa da wariyar launin fata a Amirka musamman wacce 'yan sanda ke nuna wa bakar fata a kasar, Shugaba Donald Trump ya gudanar da garanbawul ga dokar tsarin aikin 'yan sanda a kasar. kwaskwarimar da ya yi wa dokar ta tanadi hamata wa 'yan sanda shake mutun a lokacin kama shi sai dai in ya kasance barazana ga rayuwar dan sandan.

 Shugaba Trump wanda ya gana da wasu daga cikin iyalan  da 'yan sanda suka kashe masu mutum, ya ce  ya yi wa dokar tsarin aikin 'yan sandan gyaran huska da nufin kusanto 'yan sanda da al'umma da kuma samar da makoma ta gari ga dukkan kabilu da mabiya mabanbantan addinai na kasar.