1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Dan bindiga ya halaka mutane 12

Gazali Abdou Tasawa
November 8, 2018

A Amirka wani dan bindiga ya halaka mutane 12 da suka hada da dan sanda daya a jiya Laraba bayan da ya buda wuta kan taron jama'a a wani gidan rawa na kusa da birnin Los Angeles kafin daga baya ya bindige kansa. 

https://p.dw.com/p/37to5
USA Schießerei Thousand Oaks Kalifornien
Hoto: Reuters/N. Steinwender

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharin wanda ke da kasunba sanye da rigar sanyi baka dauke da babbar bindiga kuma ya fara ne da buda wuta kan mai gadin kofar gidan rawan da kuma wata mata mai sayar da tikitin shiga kafin ya kutsa a cikin gidan rawan ya buda wuta kan jama'a.

Kwamishinan 'yan sanda birnin Ventura ya ce akwai kuma mutane da dama da suka ji raunika da yanzu haka aka kwantar da su a gidajen assibiti dabam-dabam na birnin. Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance asalin mutuman da ya kai harin ba da ma dalillansa na kai harin ba.