Amirka da Katar za su yaki ta′addanci | Labarai | DW | 11.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Katar za su yaki ta'addanci

Kasashen Amirka da Katar sun amince da yarjejeniyar da zai yaki ta'addanci, yarjejeniya ya samu kwarin guiwa ne daga wani taron da ya gudana a birnin Riyadh da ya kudurci kauda tsauraran akidu da ta'addanci a doron kasa.

Mohammed bin Abdulrahman Al Thani (picture alliance/AP Photo/B. Hussein)

Firaiministan Katar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani.

Firaiministan Katar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya nuna gamsuwa kan rawar da Amirkan ke takawa na shiga tsakanin ta da sauran takwarorinta da suke takun saka. A yanzu dai Katar ce kasa ta farko a daular larabawa da suka cimma yarjejeniya mai karfi da Amirka na aza tubalin yakar tsauraran akidu da ayyukan ta'addanci.

A farkon makonnanne sakataren Amirka Rex Tillerson ya fara ziyarar rangadi a kasashen yankin larabawa, da nufin shiga tsakanin rikicin kasashen bisa zargin tallafawa ta'addanci da ake wa Katar kallo da shi.