Amirka: Blinken zai ziyarci Afirka | Labarai | DW | 12.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Blinken zai ziyarci Afirka

A mako na gaba ne Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken zai fara ziyarar aiki a kasashen Kenya da Najeriya da kuma Senegal da ke nahiyar Afirka.

A birnin Nairobi na kasar Kenya, Blinken zai gana da shugaba Uhuru Kenyatta don tattauna matakin kawo karshen annobar coronavirus da kuma batun tsaro a kasashen Habasha da Somaliya da kuma Sudan, kasancewar Kenyar na zama mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

A cikin makon Blinken zai isa Najeriya don tattaunawa da shugaba Muhammadu Buhari kan hadin gwiwa a fanonnin tsaro da fadada samun makamashi da farfado da dimokradiyya. Yayin da a Dakar, sakataren zai gana da shugaba Macky Sall na Senegal kan jaddada hadin gwiwar kasashen biyu.