Amirka: Blinken ya fara ziyara a Afirka | Labarai | DW | 17.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Blinken ya fara ziyara a Afirka

Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya fara ziyarar aiki a nahiyar Afirka da nufin tattauna kan batutuwan da suka shafi cigaban dimokradiyya.

Blinken zai kuma tattauna kan batun sauyin yanayi da rikicin kasashen Habasha da Sudan da kuma yadda za a inganta samar da allurara rigakafin annobar corona a nahiyar, lamarin da ke kasancewa fatan shugaba Biden na kerewa kasar China da ke tabbatar da ingancin nata. 

Baya ga kasar Kenya da ya isa, ana sa ran daga bisa zai je Najeriya da ke zama kasa mafi yawan al'umma a nahiyar da kuma kasar Senegal. Blinken dai na kokarin nuna bambancin gwamnatin kasar a yanzu da ta tsohun shugaban kasar Amirka Donald Trump wanda ke zama shugaba daya tilo cikin shekaru da bai kai ziyara nahiyar ba, ya kuma tozarta bakin haurenta.