Amirka: Biden zai kara wa attajirai haraji | Labarai | DW | 29.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Biden zai kara wa attajirai haraji

Shugaban Amirka Joe Biden ya ce kasar ta sake farfadowa har ma ta bude sabon babi na kokarin dakile annobar corona da ta kawo mata cikas.

Shugaban na Amirka ya fadi haka ne a yayin da yake jawabin cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin kasar ga 'yan majalisun kasar.

A cikin jawabinsa na ranar Laraba da daddare, Biden ya bukaci majalisar da ta aiwatar da gyaran fuska ga aikin 'yan sandan kasar kafin ranar 25 ga watan gobe lokacin da za a cika shekara daya da mutuwar da bakar fatar nan George Floyd ya yi a hannun dan sanda farar fata. Kazalika Biden ya sha alwashin kara haraji ga attajiran Amirka, yana mai cewa zai yi haka ne don bunkasa tattalin arzikin kasar ba wai don cin mutumcin wani ba.

Shugaban na Amirka bai kammala jawabin nasa ba, sai da ya tabo batun zaman doya da man-jar da kasar ke yi da China, inda ya ce Amirka na maraba da gogayya da China a wurin neman kasuwa a duniya. Sai dai ya ce Amirka ba ta neman China da rikici.