Amirka a sabon yaki da sauyin yanayi | Labarai | DW | 03.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka a sabon yaki da sauyin yanayi

"Yanayin muhallinmu na sauyawa, yana sauyawa ta yadda yake zama barazana ga tattalin arzikinmu da lafiyarmu".

USA Obama zu Einigung Iran Nuklearprogramm

Shugaba Obama na Amirka

Shugaba Barack Obama ya bayyana aniyarsa ƙarara kan yaki da sauyin yanayi. Cikin wani sako da aka yadda a shafukan sada zumunta ta kafar intanet, shugaba Obama ya bayyana wannan aniya a matsayin babban mataki da ya ɗauka kan yaki da sauyin na yanayi.

Ya ce "Yanayin muhallinmu na sauyawa, yana sauyawa ta yadda yake zama barazana ga tattalin arzikinmu da lafiyarmu, ya ce wannan ba a ra'ayina ba ne, abu ne da ke a zahiri idan kun amince kamar yadda na amince, ba za mu lalata wannan duniya tamu ba ta yadda 'ya'yanmu da jikoki za su koka da halayyarmu ta lalata muhalli yadda ba zai iya gyaruwa ba". A nan sai shugaban ya buƙaci isar da wannan sako ga abokai da 'yan uwa da sauran iyala.

Shugaba Obama ya ce babu ƙa'ida kan abin da gwamnatin ƙasar ta Amirka za ta gindaya na wani adadi da za ta ci gaba da ragewa na iskar carbon da kan gurbata muhalli daga cibiyar samar da makamashi ta kasar wacce ke zama mafi girma ta inda Amirka ke fitar da nau'oin iskar gas da kan illata muhallin dan Adam.Da fari dai ƙasar ta sanya a gabanta cewa za ta rage isar ta Carbon da adadin da ya kai 32 cikin dari nan da shekarar 2030 dan koma wa amfani da makamashi da ake iya sabintawa.