Amincewa da sabon kundi a Zimbabwe | Labarai | DW | 19.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amincewa da sabon kundi a Zimbabwe

Al'ummar Zimbabwe ta zaɓi a aiwatar da tanadin sabon kundin mulkin ƙasar wanda ke samun goyon bayan duk ɓangarorin gwamnati, wanda kuma zai share fagen gudanar da zaɓe

Zimbabwe President Robert Mugabe, left, talks to Morgan Tsvangirai, Zimbabwe Prime Minster after the swearing in ceremony of new ministers at State House in Harare, Thursday, June, 24, 2010. (ddp images/AP Photo/Tsvangirayi Mukwazhi)

Robert Mugabe da Morgan Tsvangirai

Al'ummar Zimbabwe ta amince da sabuwar kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda ya rage ikon shugaban ƙasa, ya kuma daɗa kai ta kusa da gudanar da zaɓe. Hukumar zaɓen ta ce kusan kashi 95 cikin 100 na al'ummar suka goyi bayan amince da sabon kundin, wanda ya sami goyon bayan shugaban ƙasa Robert Mugabe da Frime Minista Morgan Tsvangirai, manyan abokan hammayar siyasa a ƙasar, waɗanda aka tilasta masu raba iko bayan zaɓen ƙasar na shekara 2008.

Fitowar waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a sama da milliyan shida ya wuce adadin da aka zata tun farko, kuma masharhanta na hasashen cewa waɗanda zasu fito yin zaɓe lokacin zaɓukan ƙasar da za'a gudanar a ƙarshen wannan shekarar ma zasu fi haka, a abunda suke ganin zai zama tamkar wani fito na fito tsakanin Mugabe da Tsvangirai.

Sabon kundin dai ya tanadi wa'adin shekaru biyar sau biyu ma kowani shugaban ƙasa. Frime Minista Tsvangirai yayi maraba da wannan ci-gaba da ya samu ga kuma ƙarin bayanin da ya yi.

"Wannan sabon kundin tsarin mulkin jinjiri ne na gwagwarmayar demokraɗiyar zimbabwe, kasancewarsa jinjirinmu ne duk wani wanda yayi abun da ya saɓa da tanadinsa zai fuskanci shari'a"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar