Lafiya
Tallafawa marasa lafiya ta shafukan sada zumunta
February 21, 2020Talla
Matasa da dama a Najeriya kan yi amfani da shafukansu na sada zumunta don agazawa wanda ke jinya kuma basu da wadatattun kudi na sayen magani. Fauziyyah D. Sulaiman na daga cikin wanda suka yi fice a wannan harka a jihar Kano da ke arewacin kasar. Ta na da mabiya dubu 160 a shafinta na Instagram, sannan rubutunta na neman taimako ga marasa lafiya kan kai ga mutane 5000 a shafin facebook a cikin kankanin lokaci. Ta ce burinta shi ne ta yi amfani da yawan jama’anta a intanet wurin ceton rayukan jama’a. Ta yi mana bayanin yadda aikin nata ke gudana kuma za a iya saurarar cikakken shirin a nan kasa.