1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan takar 36 za su Madagaska

Philipp Sandner
November 6, 2018

A wannan Larabarce al'ummar Madagaska za su kada kuri'ar zaben sabon shugaban kasa tsakanin 'yan takara 36 ciki har da tsofaffin shugabannin kasa da gwamnati

https://p.dw.com/p/37jb1
Madagaskar Präsident Hery Martial Rakotoarimanana Rajaonarimampianina
Hoto: Reuters

Tsibirin Madagascar na a cikin yanayi na gaba kura baya siyaki, saboda tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 1960, kasar bata sami damar fitar da kanta daga kangin talauci ba.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewar kashi tara cikin goma na al'ummar kasar na rayuwa hannu baka hanu kwarya. Wannan mawuyacin halin rayuwa ya fi kamari a yankunan karkara saboda zaman kashe wando da ya yi kanta. Romeo Razafintsalam wanda ke fafutukar inganta harkokin siyasa a Madagasacar ya ce matsaloli da dama ne ke hana ruwa guda a wannan tsibiri.

"Matsalar tsaro na a sahun farko a cikin ababen da ke gurbata yanayin rayuwa a Madagaska, sai kuma tsananin talauci da kuma uiwa uba cin hanci da rashawa da ke haddasa wasu jerin bala'o'i"

Madagaskar Wahlen Kandidat Rajoelina
Dan takara Andry Rajoelina (tsohon shugaba)Hoto: Getty Images/AFP/Rijasolo

A wannan yanayi na gaba kura ne, 'yan takarar 36 ke zawarcin mukamin shugaban kasa a madagasaka, dukkaninsu maza, ciki har da wasu tsoffin shugabannin kasa da na gwamnati. Marcus Schneider, shugaban reshen madagasaka na gidauniya Friedrich Ebert Foundation, ya danganta abin da ke faruwa da  "zabe da zai shiga cikin tarihi" saboda yawan wadanda suka taba dandana dadin mulki da ke fafatawa tsakaninsu.

"Mutum zai iya kiran wannan zabe da zaben karni. A karon farko cikin tarihin Madagaska, tsoffin shugabannin kasa hudu da kuma tsoffin Firaministoci uku za su kasance cikin 'yan takara 36 da aka amince da su."

Shugaba mai barin gado Héry Rajaonarimampianina da kuma wanda ya gada Andry Rajoelina na daga cikin 'yan takarar da ake kyautata wa zaton lashe zaben, baya ga tsohon shugaba Marc Ravalomanana. Dukkanin 'yan takarar sun karkata manufofinsu ne kan hanyoyin yaye talaucin da ke addabar talakawa.