1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da kayan kamshi a gaba

Zulaiha Abubakar AMA
November 15, 2019

Shirin lafiya jari ya duba yadda mata ke amfani da wasu sabulai ko turaruka don tsafta a gabansu, ba tare da tuntubar likitocin kula da lafiyar al'umma ba don fahimtar yadda ya kamata su yi.

https://p.dw.com/p/3T5w9

Dr. Maryam Abubakar kwararriyar likita ce a Najeriya da ta bayyana muhimman hanyoyin da suka dace mata su bi su don amfani da wadannan sanadarai da ke tattare da hadura, musamman ma idan aka yi la'akari da yadda wasu lokuttan matan ke cusa ababen da basa da tabbas kan yadda aka sarrafa su a cikin jikinsu. Ku saurari shirin na Lafiya Jari don jin karin bayani da ma wasu muryoyi da dama da ke karin haske kan wannan batu na amfani da sabulai da sauran kayan kanshi da mata ke yi a gabansu.