1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 40 a Mozambik

January 28, 2013

Mutane 150,000 sun rasa muhallinsu a Mozambik sakamakon ambaliyar ruwa da ta addabi mazuana yankunan kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/17StW
Hoto: GIZ

Mummunar ambaliyar ruwa a kudancin kasar Mozambik ta tilasta wa mutane akalla dubu 150 ficewa daga wannan yanki, inji Majalisar Dinkin Duniya ta na mai gargadi da cewa yawan mutane dake barin wannan yanki ka iya karuwa. Mai magana da yawon Majalisar ta Dinkin Duniya Patricia Nakell ta fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa adadin a hukumance shi ne mutane dubu 150 suka rasa muhallinsu a lardin Gaza, sakamakon ambaliyar ruwan da ta addabi wannan yanki na kwari dake kudancin kasar. Yanzu haka dai mutanen yankin sun koma kan yankuna masu tuddai. Sai dai har yanzu hukumomi ba su san yawan mutane da ruwan yayi wa kawanya a yankunan karkara ba, inda masu ba da agajin gaggawa ke kokarin samun hanyoyin shiga. Ambaliyar ruwan ta halaka mutane 40, sannan an yi hasashen samun ruwan sama mai yawa a wasu sassa daban na kasar. Hukumomi sun yi kira ga mazauna yankunan da ake samun ruwan saman yanzu da su fice in ba haka ba za a yi amfani da karfi don kwashe su daga yankunan.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe