Ambaliya: Birtaniya za ta aika da karin sojoji | Labarai | DW | 28.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya: Birtaniya za ta aika da karin sojoji

Firaministan Birtaniya David Cameroon ya bada sanarwar aikawa da karin sojoji 200 domin kawo dauki a yankunan arewacin kasar da suka fiskanci ambaliya

Firaministan Birtaniya David Cameron ya bada sanarwar aikawa da karin sojoji 200 domin kawo dauki a yankunan Arewacin kasar da suka fiskanci ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kama da bakin kwarya da aka share kwanaki ana shatatawa a yankin.

Da ma dai a baya gwamnatin ta aika da sojoji 300, amma kuma Firaminista Cameron ya ce akwai yiwuwar tura karin wasu sojojin dubu idan dai har matsalar ta kara kamari a nan gaba.

Kafofin yada labaran kasar ta Birtaniya dai sun ruwaito cewa a wannan Litinin Firaministan Cameron zai kai ziyara a yankunan da ambaliyar ta shafa.