Al′ummar Mauritania na gudanar da zaɓe | Labarai | DW | 23.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Mauritania na gudanar da zaɓe

Duk da cewa jam'yyun adawa da dama sun yi ƙauracewa zaɓen, na 'yan majalisa da ƙananan hukumomi, mahukuntan ƙasar sun cigaba da gudanar da shi

A wannan Asabar din ce al'ummar kasar Mauritania ke gudanar da zaben 'yan majalisun dokoki da na kananan hukumomi, zaben da ke zaman irinsa na farko cikin shekaru bakwai din da suka gabata.

Kimanin mutane miliyan uku da kusan rabi ne dai za su jefa kuri'unsu a zaben wanda jam'iyyun adawa suka ce sun kauracewa saboda a cewarsu ba za su ga alamar za a yi adalci a zaben ba.

To sai dai yayin da jam'iyyun adawa suka kauracewa zaben na yau, jam'iyyar Tewassoul wadda ita ma ta adawa ce kuma ta ke da alaka da kungiyar nan ta 'yan uwa Musulmi ta ce za ta shiga a dama da ita a zaben don bada gudumawarta wajen kawar da gwamnati mai ci yanzu.

Hasashen da aka yi dai gabannin fara zaben ya nuna cewar jam'iyyar UPR ta shugaba kasar mai ci Mohamed Ould Abdel Aziz za ta samu rinjaye a zaben na yau wanda ke cike da takaddama.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Pinaɗo Abdu Waba