1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Tsadar rayuwa saboda takunkumi

January 27, 2022

Farashin kayayyakin bukatun yau da kullum sun yi tashin gwaron zabi a Mali, kwanaki kalilan bayan da ECOWAS ko CEDEAO ta sanya takunkumin karya tattalin arziki ga kasar.

https://p.dw.com/p/46CcG
Ghana Accra | Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma | ECOWAS
Taron kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, ya amince da saka takunkumi ga MaliHoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Tuni dai al'ummar kasar ta Mali suka shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon karancin kudi da suke fama da shi. Kafin ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa Mali takunkumi dai, 'yan kasar na sayan kilo daya na sukari a kan FCFA 500. Amma a yanzu farashin yana hauhawa, inda a wasu wurare ake sayan sukuri a kan kudi 600 zuwa 750 na FCFA din. A hakikanin gaskiya ma dai, kusan farashin dukkanin kayayyakin bukatun yau na ci gaba da hauhuwa, sakamakon yadda 'yan kasuwa ke boye hajarsu domin samun kazamar riba.

Karin Bayani: ECOWAS ta saka takunkumi ga gwamnatin Mali

Kananan 'yan kasuwa, na fahimtar hali na tsaka mai wuya da al'ummar Malin suka tsinci kansu a ciki. Amma sun nunar da cewa dole ne su kara farashin kayayyki, domin su ma da tsada suke sara. Sai dai hujjar da 'yan kasuwar ke bayarwa na da daure kai, saboda kayan abinci da ake da matukar bukata ba sa cikin abubuwan da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta sanya takunkumi a kansu.

Mali Assimi Goita ne jagoran juyin mulki
Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali, sun gaza cimma wa'adin ECOWAS ko CEDAOHoto: Annie Risemberg/AFP/Getty Images

Ko da Hukumar da ke Kula da Cinikayya da Kayyade Farashi a Malin, sai da ta ce babu wata hujjar samun hauhawar farashi a kasuwanni. Don haka, akwai wasu dalilai na dabam da ke haifar da hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwannin Mali. Wasu sun ambaci tarnaki da saka samu a kan hanyar da ke hade Bamako da birnin Dakar na Senegal, wanda ke haifar da sarkakiyar jigilar kayayyaki. Yayin da wasu kuma ke dora alhaki a kan 'yan kasuwa da ke boye hajojinsu.

Karin Bayani: ECOWAS ko CEDEAO ta sakawa Mali takunkumi

Tuni al'umma a Mali suka fada cikin wahala, saboda farashin sauran kayan ma na karuwa bayan da sojoji suka gaza cimma wa'adin ECOWAS na mika mulki ga gwamnatin farar hula. Farashin tan din siminti wanda shi ke karashin takunkumi alal misali, ya tashi daga 95,000 FCFA yanzu zuwa 130,000 FCFA a wasu wurare tun bayan rufe iyakokin kasar. Kasar Mali na shigo da kaso 65 cikin 100 na kayan bukatunta na siminti, daga tashar jiragen ruwa ta Dakar da ke kasar Senegal. Sai dai a game da kayan abinci da ba a saka takunkumi a kansu ba, doka ta tanadi ladabtar da 'yan kasuwa da suka ki amfani da farashin da hukumomin Mali suka kayyade.