1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Madagaska na zaben shugaban kasa

Yusuf Bala Nayaya
November 7, 2018

Tun da misalin karfe shida wasu masu zaben suka fita tashoshin kada kuri'a a birnin Antananarivo baban birnin kasar ta Madagaska.

https://p.dw.com/p/37nhR
Madagaskar Wahlen
Hoto: Reuters

Miliyoyin al'ummar kasar Madagaska tun a safiyar wannan Laraba sun fita tashoshin kada kuri'a don zaben shugaban kasa a wannan kasa da ke zama tsibiri a Tekun Indiya wacce ke fama da tarin matsaloli na rashin aiyuka da talauci da cin hanci da rashawa.

Tun da misalin karfe shida na safiyar Laraba wasu masu zaben suka fita tashoshin kada kuri'a a birnin Antananarivo don zaben daya daga cikin 'yan takara 36 da suka hadar da shugaba mai ci Hery Rajaonarimampianina da tsofaffin shugabannin kasar ta Madagaska biyu wato Marc Ravalomanana and Andry Rajoelina.