Al′ummar Liberiya za su zabi sabon shugaba | Labarai | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Liberiya za su zabi sabon shugaba

A wannan Talatar ce al'ummar Liberiya za su kada kuri'a don zaben sabon shugaban kasa bayan da wa'adin shugaba mai ci Ellen Johnson Sirleaf ya kawo karshe.

Liberia Wahlen in Monrovia (DW)

'Yan takara da dama ne dai ke zawarcin kujerar Sirleaf ciki kuwa har da shararren dan kwallon kafar nan George Weah da dan majalisar dattawa kana tsohon madugun 'yan tawayen nan Prince Johnson, wanda mayakansa suka hallaka Samuel Doe. Gabannin yin zaben wanda za a yi shi tare da na 'yan majalisar dokoki, wasu 'yan takarar shugabancin kasar ciki kuwa har da Benoni Urey sun ce ba za su amince da sakamakon zaben ba muddin bai gudana cikin tsari da aminci ba. Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 70 da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata gwamnati ta farar hula a kasar wadda a baya ta fuskanci yakin da daidaita ta.