Al′ummar Cote d′Ivoire sun fita kuri′ar raba gardama | Labarai | DW | 30.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Cote d'Ivoire sun fita kuri'ar raba gardama

Masharhanta da 'yan adawa na baiyana sabon kundin tsarin mulkin da za a kada kuri'a a kansa a matsayin mai matukar hadari da daure kai, suna masu cewa ya saba da tafarkin dimokradiyya.

Elfenbeinküste Präsident Alassane Ouattara (Reuters/L. Gnago)

Kuri'ar raba gardama mai cike da suka a kasar Ivory Coast

A ranar Lahadin nan ce al'ummar Cote d'Ivoire suka fita don kada kuri'a a zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki wanda Shugaba Alassane Ouattara ya dage cewa zai hada kan kasar da ke fama da rikici. Sai dai kuma tuni masharhanta da 'yan adawa ke baiyana sabon kundin tsarin mulkin a matsayin mai matukar hadari da daure kai, suna masu cewa ya saba da tafarkin dimokradiyya. Wasu na ganin tsarin a matsayin wata hanya ga shugaban ta neman dawwama a kan mulki.

Masu rubuta sharhi dai a kasar ta Cote d'Ivoire sun bayyana kokwanto kan fita kada kuri'ar  sannan ba su da kwarin gwiwa ko sauyin zai samu amincewa.

Shugaba Ouattara dai karkashin wannan sauyi na kundin tsarin mulkin kasa zai ba shi dama ta zabin mataimakinsa sannan yana da ta cewa a kafa majalisar dokoki.