Al′ummar Botswana na zaben ′yan majalisa | Labarai | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Botswana na zaben 'yan majalisa

Masu lura da al'amura a kasar ta Bostwana na ganin cewa jam'iya mai mulki za ta taka rawar gani a wannan zabe duk kuwa da zarge-zagen da 'yan adawar kasar suka yi.

Ian Khama

Shugaban kasar ta Bostwana Ian Khama da ya kada kuri'ar sa tun da sanyin safiya a birnin Serowe dake a nisan km 300 da Gaborone babban birnin kasar, ya samu gaisawa da dumbun magoya bayan sa kafin daga bisani yayi maza ya fice daga wurin.

Zaben dai na gunada cikin tsanaki a duk fadin kasar a cewar kakakin hukumar zaben kasar ta Bostwana Osupile Maroba inda a kalla 'yan kasar dubu 824 ne zasu kada kuri'un su a wannan rana, inda za su zabi 'yan majalisun, wadanda daga bisani su kuma su zabi shugaban kasar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar, kuma ana ganin cewa shugaban mai ci yanzu zai iya samu wani wa'adi na biyu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba