Al′ummar Amurika na yin zaman makoki | Labarai | DW | 15.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Amurika na yin zaman makoki

Bayan da wani ɗan bindiga ya kashe wasu yan makaranta guda 20 tare da wasu mutane takwas a jihar Connecticut

Shugaba Barack Obama na Amurika ya baiyana alhininsa da juyayi sakamakon kisan da wani dan bindiga ya aikata, a cikin wata makarantar da ke a garin Newtown cikin jihar Connecticut inda ya kashe yara guda 20 yan shekaru biyar zuwa goma tare da wasu mutane guda shida.

Shugaba Obama dai ya isar da ta'aziyarsa ga iyalen waɗanda lamarin ya rutsa da su, sannan kuma ya ba da ummarni da a yi ƙasa ƙasa da tutar ƙasar a matsayin zaman makoki.Wanda ya aikata ta'adin da ake kira da sunnan Adam Lanza ɗan shekaru 20 da haifuwa,masu aiko da rahotanin sun ce gabannin ya buɗe wuta a kan mutanen sai da ya kashe maihafiyarsa wacce mai koyar wa ce, a makarantar ta Sandy.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita :Saleh Umar Saleh