1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar ƙasar Kwango na neman ɗauki

October 9, 2013

Ɗaruruwan mutane da suka ƙauracewa gidajensu a Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango, sakamakon yaƙi tsakanin gwamnati da 'yan tawayen M23 na cikin ƙunci.

https://p.dw.com/p/19wmS
Hoto: Phil Moore/AFP/Getty Images

Tawagar Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta kai ziyara zuwa arewacin garin Kivu, na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango inda al'ummar yankin suka warwatsu sakamakon rikici tsakanin gwamnatin ƙasar da 'yan tawayen M23.A yayin ziyarar tawagar, sun gana da mahukuntan Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, tare da tattauna batun ayyukan rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD da a yanzu haka ke taimaka wa dakarun Kwango wajen fatattakar 'yan tawayen M23 da suke yaƙar gwmnati.

Kongo Frauen
Wasu daga cikin matan da suka rasa mazajensu sakamakon yaki tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen M23 a Kongo.Hoto: Phil Moore/AFP/Getty Images

Daga bisani tawagar ta ziyarci wasu daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira da yaƙi ya tilasta wa barin gidajensu, inda suka tattauna da wasu daga cikin matan da aka kashe musu mazajensu da 'ya'yansu sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin gwamnati da ƙungiyar 'yan tawaye ta M23. Wasu daga cikin matan cikin sun bayyana wa tawagar halin da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon wannan yaƙi.

Buƙatar samar da zaman lafiya a Kongo

Ta ce: "Mun saba da ganin jajayen fata suna zuwa daga gurare daban-daban ba tare da sun kawo mana ɗauki ba, sai dai mun ji cewa kuna da ƙarfin kawo mana zaman lafiya. Ba mu da mazaje, ba mu da 'ya'ya, muna cikin mawuyacin hali. In mun je nemo abinci sai a tare mu a yi mana fyaɗe, wasu daga cikinmu na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, wato HIV Aids ko SIDA, da kuma wasu cututtuka da ake dauka ta hanyar saduwa". " Ku taimaka mana ku farfado mana da zaman lafiya, muna rokonku da ku taimake mu zaman lafiya ya dawo ƙasarmu"

Da yake mai da jawabi dangane da koken da matan suka yi, shugaban Kwamitin Tsaro na MDD Gary Quinlan, ya ce tabbas an sami ci gaba ta fannin zaman lafiya a ƙasar ta Kongo sai dai har yanzu a kwai sauran aiki a gaba, ya kuma ƙara karfafa musu gwiwa ta hanyar sanar da su makasudin ziyarar da suka kai.

Gespannte Lage in Kinschasa
Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya na kokarin taimakawa dakarun gwamnatin Kongo.Hoto: AP

Ƙoƙarin fatattakar 'yan tawayen M23

Ya ce "Makasudin wannan ziyara ta mu shi ne, domin mu duba halin da ake ciki ta fannin yin amfani da yarjejeniyoyin da aka cimma a Kampala da kuma Adis Ababa a kan matakan da ya kamata a ɗauka wajen fatattakar 'yan tawaye. Har yanzu akwai aiki mai yawa a gaba. Sai dai na sani cewa Kongo na kan hanyar da ta dace kuma muna muku fatan samun nasara".

Tawagar Kwamitin Tsaron na MDD da ta kai ziyara Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwangon, ta kuma tabbatarwa da dubban iyalan da suka ƙauracewa gidajensu sakamakon yakin da ake fafatawa tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar da 'yan tawayen M23 cewa, Birtaniya da Amirka sun buƙaci gwamnatin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwangon ta hukunta sojojin da ake zargi da yi wa kimanin mata da 'yan mata130 fyade, a gabashin ƙasar da yake fama da rikici.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourrahamen Hassane