Al′umma da talauci a Afirka na karuwa | BATUTUWA | DW | 11.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Al'umma da talauci a Afirka na karuwa

Al'umma a nahiyar Afirka na bunkasa cikin sauri fiye da kima. A kan alakanta hakan da yawan 'ya'ya da ake haifa a nahiyar. A kasashen nahiyar da dama, tattalin arzikinsu ba ya isar yawan al'ummar da suke da ita.

Trinkwassser an Schule in Burundi (picture-alliance/dpa/T. Schulze)

Haihuwa barkatai na daga cikin abin da ke janyo karuwar al'umma da talauci a Afirka

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta ware ranar 11 ga watan Yuli na kowacce shekara, domin wayar da kan mutane kan illa da kuma kalubalen da ke tattare da yadda al'umma ke yawaita a duniya. A nahiyar Afirka an fi fuskantar irin wadannan matsaloli, inda ga misali ko da batun lura da lafiya da kuma ilimin yaran da akan haifa da zasu zama manyan gobe ba a shirya masa ba. Koda yake a yanzu an dan samu saukin mutuwar yara kanana idan aka kwatanta da shekarun baya, godiya ta tabbata ga samar da magunguna da aka yi wadanda ke magance cututtukan da ke saurin hallaka yara kanan. Wannan ci-gaba har a nahiyar Afirka ya samu matuka. To amma duk da irin wannan ci-gaban, har yanzu a nahiyar Afirka ana haifar 'ya'ya barkatai, inda aka yi kiyasin a kan haifi kimanin yara biyar a wasu gidaje da za a iya cewa ba su haifi yara da yawa ba. Alisa Kaps jami'a ce a cibiyar bunkasr al'umma da ci-gaba a Berlin fadar gwamnatin Jamus. Ta bayar da misalin irin bunkasar jama'a da ake samu a nahiyar Afirka. 

Kinder in einem Flüchtlingslager in Äthiopien nahe der Grenze zum Südsudan (DW/Fanny Facsar)

A Afirka a kan haifi yara a bar su suna gararanba

"Bunkasar al'umma a Afirka na matukar sauri. Izuwa shekara 2050 al'ummar nahiyar Afirka za ta rubanya sau biyu. Daga miliyan dubu100 da miliyan 300 zuwa miliyan dubu 200 da miliyan 500. Wannan karuwar ta yi yawa matuka idan mutum ya duba dai-daikun kasashe misalin Jamhuriyar Nijar. Kafin nan da shekaru 30 al'ummar Nijar za ta rubanya har sau uku. Duk da saurin bunkasar jama'ar da ake samu, babu kayan more rayuwa, misali hanyoyin sufuri da asbitoci da makarantu  da guraben aiki."
 
Sai dai matsalar da ake fuskanta ita ce, yadda a nahiyar Afirka aka jahilci illar haifar 'ya'ya barkatai, a cewar masanin harkokin Afirka, Jakkie Cilliers darakta a cibiyar tsaro da ke kasar Afirka ta Kudu. Inda yace baya ga wadanda ba su yi karatu ba da ke bin al'adu hatta su kansu wasu 'yan bokon nahiyar Afirka sun dauka cewar bunkasar al'umma shi ne zai kawo bunkasar tattalin arziki, wannan kuwa wata matsalace da bangaren shugabannin addini da ke adawa da ba da tazarar haihuwa ke janyowa. Sai dai akwai kasashen da aka samu ci gaba wajen kayyade iyali a nahiyar ta Afirka. Misali kasashen Afirka ta kudu da Masar suna cikin kasashen da ba a cika haihuwar 'ya'ya barkatai ba, kuma ba su kasance kasashen da suka fi talauci a nahiyar ba. To amma a cewar masanan ko da a wadannan kasashen biyu ana fama matuka da rashin aikin yi ga matasa. 

Sauti da bidiyo akan labarin