Al′umar Kano na alhinin rasuwar dan Masani | Zamantakewa | DW | 03.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Al'umar Kano na alhinin rasuwar dan Masani

Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule ya rasu bayan gajeriyar jinya a wani asibiti a Masar.

Allah ya yiwa Danmasanin Kano Alhaji Maitama Sule rasuwa.

Ya rasu a yau litinin a wani asibitin birnin Alkahira a kasar Masar inda ya je jinya.

A na sa ran dawo da gawarsa inda za'a yi masa jana'aiza a fadar mai martaba Sarkin Kano a gobe talata idan Allah ya kaimu.

Mairigayi Danmasanin Kano Alhaji maitama Sule ya rike mukamai da dama da suka hada da Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya da kuma ministan ma'adanai da wutar lantarki a zamanin jamhuriya ta farko. 

Ya rasu yana da shekaru 87 a duniya. Gwamnatin jihar Kano ta ware gobe Talata a matsayin ranar hutu don zaman makoki da girmamawa ga marigayin.