1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah ya yi wa George H.W. Bush rasuwa

Ahmed Salisu
December 1, 2018

Rahotanni daga Amirka na cewar tsohon shugaban kasar George Herbert Walker Bush ya rasu.

https://p.dw.com/p/39Ffi
Ex-US-Präsdient George H.W. Bush gestorben
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Jackson

Wani sako da iyalansa suka fidda ta shafin Twitter ya ce tsohon shugaban kasar ya rasu ne a jiya Juma'a ya na da shekaru 94 da haihuwa. Shugaban wanda ya mulki Amirka daga shekarar 1989 zuwa 1993 ya rasu ya bar 'ya'yansa biyar ciki kuwa har da George W. Bush wanda shi ma ya mulki kasar ta Amirka. Na gaba ne kadan ne ake sa ran iyalansa za su bayyana lokacin da za a yi masa jana'iza. Tuni da shugabannin duniya da ma Amirka suka fara aikewa da sakonninsu na ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban wanda da dama daga cikinsu suka ce rashin ya haifar da wani gibi da zai yi wuyar cikewa.