Alkaluma da bayanai dangane da kakar Bundesliga ta shekarar 2019/20
Sabbin 'yan wasa, sabbin masu horas da 'yan wasa, akwai dai kallo da zai biyo baya a sabuwar kakar wasannin Bundesliga.
Wadannan Klub din Bundesliga bakwai suna da sabon mai horaswa
Klub bakwai za su shiga kakar bana da sabbin masu horaswa. Leipzig Julian Nagelsmann shi ne ka'dai ke da da kwarewa kan Bundesliga, Hoffenheims Alfred Schreuder da kuma Ante Covic na Hertha, da ma can suna da mataimaka ne a klub din. Schalke David Wagner, FC Köln Achim Beierlorzer da Gladbach Marco Rose sun taba ba da horo a wasu kananan klub. Wolfsburg Oliver Glasner sabon zuwa ne.
Jamus ta kasance daya daga cikin lig biyar mafi zura kwallaye a Turai.
Da kwallaye 973 a wasanni 306 na Bundesliga a bara, haka ya sa Jamus ta kasance daya daga cikin lig biyar mafi zura kwallaye a Turai. A wasanni 24 an zura kwallaye kimanin 10 - hakan yasa kakar bara ta kasance wace aka fi zura kwallaye cikin shekaru biyar da suka gabata. Ko yaya za ta kasance a bana? lokaci ne zai nuna.
Euro Milion 80 - shi ne dan wasa mafi tsada a tarihin Bundesliga
Bayern München sun rubanya kudin don sayo Lucas Herández daga Atletico Madrid. Dan Kasar Faransa da ke wasan baya in ya samu sauki daga raunin da ya samu a kafa zai yi aiki tare da Niklas Süle a tsare baya. Amma yawan tarihin zai rubanya in har Bayern ta samu nasarar sayo Leroy Sane daga Manchester City.
Zura kwallaye kamar almara sai Paco Alcacer
Dan kasar Spain wanda farkon wasanninsa da Bundesliga ya samo wa Borussia Dortmund kwallaye 18, hakan ya kara yawan kwallayen Bundesliga bayan wasanni uku. Bayan warkewa daga raunin hannu da kafa da ya samu, Alcacer ya nuna bajintarsa. wannan zai zame koma baya ga BVB tare da Julian Brandt da Thorgan Hazard sabbin zaratan da suka dauko.
Klub uku suka haye zuwa Bundesliga a bana
A karon farko tun kakar 2012/13 a bana sabbin kungiyoyi uku suka haura rukunin Bundesligar: Sune FC Köln,da SC Paderborn da kuma Union Berlin. da FC Köln sun je kasa ne a kakar daya kawai. SC Paderborn sun hauro kai tsaye daga rukunin na 3. su kuwa Union Berlin wannan shi ne karon farko da za su shiga wasannin Bundesliga a tarihin kungiyar.
1977 -karshe Berlin-Derby a Bundesliga
Bisa haura rukunin Bundesliga da Union Berlin suka yi, hakan ya nuna babban birnin kasar a shirye suke, inda a karon bayan kusan shekaru 40 Berlin-Derby sun shiga murza leda a Bundesliga. Lokaci na karshe da Berlin ya kawo klub biyu shi ne a ranar 4. ga watan Aprilu na shekara 1977. A wancan lokacin Borussia da Hertha Berlin BSC sun tashi 2:0.
Claudio Pizarro zai cika shekaru 41 a kaka'ar bana
Ko ta yaya dan Werder Bremen Claudio Pizarro zai kare sana'arsa a Bundesliga? da wasan Peru da ke buga wasan gaba, a wasannin karshe ya samar wa Werder Bremen kwallaye biyar, ya yi alkawarin yin ritaya 2020. Don haka sabuwar kaka za ta kasance ta karshen wasanninsa. Klaus Fichtel, Uli Stein da Toni Schumacher sune za kusance masu yawan shekarun Pizarro a wasannin Bundesliga.