Alkali a Guatemala ya ce a kama shugaban kasa | Labarai | DW | 03.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alkali a Guatemala ya ce a kama shugaban kasa

Shugaba Perez dan shekaru 64 da ke zama tsohon janar mai ritaya an zabe shi ne da zummar ya kawo karshen aikata cin hanci da rashawa a kasar ta Guatemala.

Guatemala Präsident Otto Pérez Molina

Otto Pérez Molina shugaban Guatemala

Wani alkali a kasar Guatemala ya bada sammaci na a tsare shugaban kasar Otto Perez a cewar ofishin atoni janar a ranar Laraba. Wannan dai na zuwa ne saboda zargin badakalar cin hanci da rashawa a gwamnatin shugaba Perez, abin da kuma ya sanya kasar cikin rudani kwanaki gabannin zaben shugaban kasa da za a yi.

A ranar Talata ce dai 'yan majalisar dokokin kasar suka cire wa shugaba Perez rigar kariya, abin da ya kara dugunzuma kasar cikin rudani ganin shugaba Perez dan shekaru 64 da ke zama tsohon janar mai ritaya an zabe shi ne da zummar ya kawo karshen aikata laifuka da yaki da cin hanci.

Tuni dai shugaba Perez ya bayyana wannan yunkuri na kama shi a matsayin yarfe na siyasa. kuma a cewar 'yan sandan kasar suna da dama ne su kama shi tsakanin karfe shida na safe zuwa shida na yamma agogon kasar ta Guatemala.