Aljeriya: An rantsar da sabon shugaba | Labarai | DW | 19.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aljeriya: An rantsar da sabon shugaba

Sabon shugaban Aljeriya ya karbi rantuswar kama aiki a wani kasaitaccen bukin da aka shirya na rantsar da shi kan madafan iko a babban birnin kasar.

Mai shekaru 74 a duniya  Abdelmadjid Tebboune ya lashe zaben shugaban kasar ne tun a zagayen farko da kaso fiye da 50 cikin dari a gaban sauran abukanin hamayarsa, kana kuma a gaban hukumomin kasar na rikon kwarya sabon shugaban ya bayyana cewa zai yi biyayya ga kundin tsarin mulkin da ci gaba da gudanar da harkokin mulki a cikin yananyi mai kyau domin ganin dorewar tsarin dimukuraiyya.

Ana hasashen tun daga wannan rana ta Alhamis, sabon shugaban zai bayaana sunan firaministansa da zai ja ragamar harkokin gwamnati, wacce za ta fuskanci kalubalai barkatai ciki har da na masu zanga-zanaga da boren kin jinin hukumomin kasar.