Ali Modu Sheriff tsohon gwamnan Jihar Borno da ke Najeriya daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2011, kuma ya yi sanata daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Ali Modu Sheriff ya yi gwamnan karkashin jam'iyyar ANPP, amma bayan sauka daga mukamin ya koma jam'iyyar PDP har ya zama shugaban jam'iyyar na kasa, duk da rudanin da ake samu, saboda lokacin da yake gwamnan a Jihar Borno aka samu rikicin Boko Haram wanda ya zama ta'addanci mafi girma a tarihin Najeriya.