Alhazai sun yi jifan shedan a Mina | Labarai | DW | 15.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhazai sun yi jifan shedan a Mina

Aikin hajji na 2013 ya kai kololuwarsa a Mina na kasar saudiyya inda alhazai suke jifan shedan da ke zama daya daga cikin shika-shikan aikin na Hajji.

Dubun dubatan Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya sun yi jifan shedan a yau talata bayan da suka yi hawan Arfa a jiya litinin. Wannan Jifa dai ya na daya daga cikin shika-shikan aikin Hajji, wanda ya wajaba a kan duk mulusmin da ke da hali. Alhazan dai wadanda aka kyasta sun kai miliyan daya da dubu 500 sun jefa duwatsu 21,wato dutse 7-7 a kan kowace jamra daya daga cikin ukkun dake jere a matsayin shedan. Jami'an tsaro da daman gaske ne ke sintiri a Minna domin kula da alhazai.

Bayan jifan shedan dai alhazai za su koma Makka inda za su yi dawafi a Dakin Ka'aba, wanda a jikinshi dutsen shan nono (Hajr Aswad) ya ke makale. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Musulmi a sassa daban daban na duniya ke Sallar Layya, ta yankan sadaka domin tunawa da lokacin da Annabi Ibrahim ya bi umarnin Allah (SWT) ya kusa yanka dansa Annabi Isma'il .

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh