Alhazai sun gudanar da jifan shaidan | Labarai | DW | 11.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhazai sun gudanar da jifan shaidan

Muslimi kimanin miliyan biyu da rabi da ke gunadar da aikin hajjin bana a wannan Lahadin sun gudanar da jifan shaidan wanda ke zama rukunin karshe na aikin Hajji.

Mahajjatan wadanda ke sanye da Harami sun yi tattaki cikin tsananin zafin rana daga Minna zuwa wurin jifan shaidan.

Hukumomin Saudiyya sun ce an zuba dubban jami'an tsaro domin tabbatar da kariyar Alhazai.

A shekarar 2015 an sami turmutsitsi a Minna a hanyar zuwa wurin jifan shaidan wanda ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu biyu.

Bayan jifan shaidan Alhazai za su koma birnin Makka domin yin tawafi.