Alhaji Atiku Abubakar zai tsaya takara a zaɓen Najeriya | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhaji Atiku Abubakar zai tsaya takara a zaɓen Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar shugabancin Najeriyar.

Alhaji Atikun wanda zai yi takarar a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta adawa ya ce ƙasar, tana buƙatar ceto daga barazanar rushewar da rashin iya shugabanci ya haifar cikin ɗan ƙanƙanen lokaci.

Ana sa ran samun takara mai zafi a tsakanin Atikun da tsohon shugaban ƙasar Janar Muhammad Buhari da kuma gwamnan Jihar kano Rabi'u Musa Kwankwaso a gwagwarmayar neman tikitin jam'iyyar ta APC da ke ƙara farin jini a sassa daban-daban na Najeriyar.