Algeriya: Bouteflika ya yi kira ga koyarwa ta gari | Labarai | DW | 07.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Algeriya: Bouteflika ya yi kira ga koyarwa ta gari

Shugaban kasar Algeriya Abdelaziz Bouteflika, ya yi kira ga kasashen Larabawa da su kara azama wajen samar da koyarwa ta gari don shayo kan matsalar tsatsauran ra'ayi da ke kai wa ga ayyukan ta'addanci.

Shugaba Bouteflika na Algeriya mai shekaru 81 da haihuwa, wanda bai cika bayyana a bainar jama'a ba tun bayan matsalar da ya samu ta bugon zuciya a shekara ta 2013, ya yi kira ga kungiyar kasashen Larabawa, da ta matsa kaimi wajen sake dora al'ummarta kan kyaukyawan ta farki na koyarwar adini, wanda ta haka ne za a iya kawo karshen tsatsauran ra'ayi da ake fusaknta na adini.

Shugaban na Algeriya ya nuna bakincikinsa kan yadda ake danganta ta'addanci da adinin Muslunci, musamman ma ganin yadda masu aikata ayyukan ke alakanta abun da suke yi da adinin na Muslunci.