1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Albert na biyu zai sauka daga karagar mulkin Beljiyam

July 20, 2013

Sarkin Beljiyam, Albert na biyu ya yi kira ga al'umar kasar da su hada kansu a wuri daya

https://p.dw.com/p/19BFo
Hoto: picture-alliance/dpa

A cikin jawabinsa na ban kwana Sarkin Beljiyam, Albert na biyu, mai shirin barin gadon sarauta ya yi kira da a samu hadin kan kasar. A cikin jawabin nasa sarkin ya ce yana da muhimmanci a tabbatar da hadin kan jihohin kasar masu tsarin federaliya. Ita dai kasar ta Beljiyam tana fama da rikici da ke tsakanin bangarenta da ke amfani da harshen Faransanci da dayan bangaren da ke amfanin da harshen Flemish. Jam'iyyar N-VA ta Flemish, wadda yanzu ke da karfi a kasar ta dasa ayar tambaya game da tsarin federaliya na masauratar kasar.

A ranar Lahadi Sarki Albert mai shekaru 79 zai sauka daga karagar mulki a hukumance. Babban dansa, Philippe shi ne zai gajeshi a matsayin sarkin kasar Beljiyam na cikon bakwai.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal