1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ouattara zai tsaya takara a zaben Oktoba

Abdourahamane Hassane MNA
August 7, 2020

Shugaba Alassane Ouattara na Côte d'Ivoire ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a wa'adi na uku a zaben shugaban kasar da za a yi a kasar a cikin watan Oktoban da ke tafe.

https://p.dw.com/p/3gaH7
Elfenbeinküste Präsidentschaftswahl Alassane Ouattara
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya yi na minitoci 25 a jajibirin bikin zagayowar cikar shekaru 60 da kasar ta samu 'yancin kai.

Ya ce ''Na yanke shawarar amsa kiraye-kirayen da 'yan kasata ke yi mani na tsayawa takara, don haka zan yi takara a zaben 31 ga watan Oktoba.''

Tun farko Alassane Ouattara ya yi furcin cewar ba zai tsaya takarar ba, to amma bayan mutuwar firaministan kasar Amadou Gon Coulibaly ya canza ra'ayi, sai dai 'yan adawa sun ce ba za ta sabu ba.