Shugaba Ouattara ya kafa jam'iyyar RHDP a Cote d'Ivoire
July 17, 2018Talla
Jam'iyyar RDR ta Shugaba Alassane Ouattara da jam'iyyar UDPCI ta Albert Toikeuse Mabri mai kujeru shida a majalisa da kuma wasu manyan 'yan siyasar kasar masu da'awar bin akidar tsohon shugaba marigayi Houhouete Boigny ne suka hade wuri daya domin kafa wannan sabuwar jam'iyya ta RHDP.
Bayan muhawara ta sama da awa daya da babban taron jam'iyyar ya gudana a birnin Abidja ya zabi Shugaba Ouattara a matsayin shugaban sabuwar jam'iyyar. Tun farko dai jam'iyyar PDCI ta Henry Konan Bedie babbar abokiyar kawancen mulki da jam'iyyar RDR ta Shugaba Ouattara ta ki amincewa da shirin shugaban na hade jam'iyyunsu wuri daya domin kafa wannan sabuwar jam'iyya.