Al′amura sun fara komawa daidai a Bangui | Siyasa | DW | 01.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Al'amura sun fara komawa daidai a Bangui

Tashin hankali ya barke inda mutane da dama suka halaka a kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan da a ranar Sallar Layya aka kashe wani matashi Musulmi dan Acaba.

Brüssel Geberkonferenz zur Zentralafrikanischen Republik (Catherine Samba-Panza)

Shugabar riko Catherine Samba-Panza

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayan tashe-tashen hankullan da aka fuskanta na tsawon kwanaki hudu sakamakon kashe wani matashi Musulmi dan Acaba da wasu mutane suka yi. Tuni dai shugabar kasar ta rikon kwarya ta dubi wannan mataki a matsayin wani sabon salo na neman mulki ta wata hanya da ba ta zabe ba.

Wai wanene yake da wata riba wajan tayar da zaune tsaye a wannan kasa ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta yaya ne kasar za ta iya fita daga cikin wannan yanayi na rikici tsakanin kabilu ko addinai, wadannan dai su ne jerin tambayoyin da hukumomin kasar na rikon kwarya suka rinka yi, inda tuni aka nuna wasu daga cikin masu neman shugabancin wannan kasa da kulla makarkashiya ta hanyar tayar da rikici a kasar.

Zentralafrikanische Republik Freilassung von Kindersoldaten

'Yan tawaye masu dauke da bindiga

Jim kadan dai bayan da ta dawo daga birnin New York na kasar Amirka, shugabar kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta rikon kwarya Catherine Samba Panza, ta ce wannan wani mataki ne na yunkurin karbar mulki da karfi.

Shugaba Samba Panza ta nuna tsaffin shugabannin kasar François Bozizé da aka hambare a watan Maris na 2013, da kuma Michel Djotodia wanda shi ne ya hambare Bozize a karkashin inuwar kungiyar Seleka kafin daga bisani sojojin Faransa na Sangaris su koresu daga birnin na Bangui a shekarar ta 2013.

Zentralafrikanische Republik Bangui Minusca UN-Truppen

Jami'an kwantar da tarzoma a birnin Bangui

Dukannin wadannan tsaffin shugabanni na samun mafaka ne a halin yanzu a wasu kasashen Afirka, amma kuma suna da fada a ji daga beangaren masu tada kayar baya a kasar, musaman ma François Bozizé da ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 10, kuma a halin yanzu ya ke son dawowa kan mulki, inda kuma a watan Agusta da ya gaba gwamnatin rikon kwaryar kasar ta yi watsi da wannan aniya ta shi ta sabili da hukuncin da ke bisa kanshi na kasa da kasa bayan da ake zarginshi da samarwa 'yan kungiyar Anti Balaka makammai a kasar, kuma lokacin da wannan rikici na baya-bayannan ya tashi, an ga 'yan Anti-Balaka da magoya bayan Bozize sun nufi fadar shugaban kasar suna kira Panza ta Sauka, Panza ta sauka daga shugabancin kasar.

To ko yaya masu lura da al'ammuran jamhuriyar Afirka ta Tsariyar suke gani kan wannan sabon yanayi? tambayar kenan da DW ta yi wa Thierry Vircoulon daraktan kungiyar International Crassis Groupe reshen Tsakiyar Afirka.

Ya ce " Ni a gani na ana magana ne da wadanda suke bayan 'yan Anti-Balaka domin tun yau da dan lokaci wasu 'yan siyasa a birnin Bangui na ta yin kiran cewa shugabar kasar ta rikon kwarya Catherine Samba Panza ta yi murabus domin a kafa wata sabuwar gwamnati ta rikon kwarya ta uku, domin a yanzu dai hana tsaya wa takara da aka yi ga wani mai bukatar takara, shi ne wanda aka yi wa tsohon shugaba Bozize wanda aka ce da zarar ya dawo kasar za'a kamashi, sannan kuma da kamun da aka yi wa Sakataren jam'iyyarsa Berthin Beya."

Zentralafrikanische Republik Proteste und Gewalt in Bangui

Masu tada zaune tsaye a Bangui

A ranar Jumma'a ce dai da ta gabata, wadda ta ke babbar rana ce ta Sallar Layya ga Musulmi, aka kashe wannan matashi a ta hanyar yanka kuma aka jefar da gawarsa a unguwar PK-5 da ke birnin na Bangui, wanda wasu ke ganin cewa hakan na da nasaba ne da bukatun da 'yan Anti-Balaka suke da na ganin Bozize ya sake dawowa kan karagar mulkin kasar.

Tashe-tashen hankullan na baya-bayannan dai ya haddasa rasuwar mutane a kalla 36 cikin kwanaki hudu, yayin da wasu mutanen dubu 30 suka bar matsigunansu domin tsira da rayuwarsu, sannan babbar kasuwar birnin Bangui ta bude kofofinta amma kuma dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na kasar Faransa na ci gaba da Sintiri a cikin Birnin.

Sauti da bidiyo akan labarin