Alamar fito na fito a ƙasar Masar
August 1, 2013Talla
A ƙasar Masar magoya bayan hamɓararren shugaba Mursi sun ci-gaba da zaman dircen da suke yi a Alƙahira babban birnin ƙasar. Masu goyon bayan Mursin dai sun ci gaba da kasancewa a dandalin da suka taru ne, duk kuwa da izinin da gwamnati ta baiwa 'yan sanda da su kawo ƙarshen gangamin da aka yi. A halin da ake ciki kuwa, yau Alhamis ne ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle zai gana da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya a birnin Alƙahira. A hirarsa da kamfanin dillalcin labaren Jamus na DPA, Westerwelle yace ƙasar Masar babbar ƙawa ce ta fannin tattalin arziki ga Jamus, kuma yace Masar wata mahimmiyar ƙasa ce a yankin Gabas ta Tsakiya bakin ɗaya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu