A Damagaram ta Jamhuriyar ana ci gaba da gudanar da al'adar tashen nan da ake yi wa lakabi da 'Asure-asure' don raya kwanakin karshe na watan azumin Ramadan. A cikin wannan faifan bidiyo Mohamed Tidjani Hassane ya duba mana yadda matasa ke gudanar da wannan al’ada ta kasar Hausa.