1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara zaben shugaban kasa a Guinea

December 28, 2025

Al'ummar Guinea na kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Lahadin nan, shekaru hudu bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula ta Alpha Conde.

https://p.dw.com/p/562L3
Zaben shugaban kasar Guinea na 2025
Zaben shugaban kasar Guinea na 2025Hoto: Abdoulaye Sadio/DW

'Yan takara guda tara ne ke fafatawa a zaben ciki har da shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Janar Mamadi Doumbouya mai shekaru 41, wanda ya yi amai ya lashe game da tsayawarsa takara kuma hasashe ke nuna cewa zai lashe zaben wanda aka haramta wa manyan 'yan adawa tsayawa takara.

Kimanin masu kada kuri'a miliyan 6.8 ne ake sa ran za su fita runfunan zaben da aka bude da kimanin karfe bakwai na wannan safiya kuma za a rufe su da kimanin karfe shida na maraicen yau.

Masu aiko da rahotonni sun ce zaben na gudana cikin tsauraran matakan tsaro, sai dai jiya Asabar jami'an tsaron kasar sun ce sun dakile 'yan wata kungiya masu dauke da makamai da ke barazanar yin zagon kasa ga tsaron kasar a unguwannin marasa galihu na birnin Conakry.

Sai dai a ranar Juma'a da ta gabata MDD ta yi Allah wadai da yanayin da aka gudanar da yakin neman zaben na Guinea musamman ma barazana da ta ce an rinka yi wa 'yan adawa.