1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-shabab ta kwace ikon wani sansanin soji

Ramatu Garba Baba
May 3, 2022

Mayakan Kungiyar Al-Shabab sun kai harin bama-bamai tare da kwace ikon wani sansanin sojin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya.

https://p.dw.com/p/4AkbM
Somalien Al-Shabaab-Kämpfer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. A. Warsameh

Jim kadan da kai harin Kungiyar al Shabaab ta fitar da wata sanarwa inda a ciki ta ce, ita ta kai wasu hare-haren bama-bamai kan wani sansanin sojin Kungiyar tarayyar Afirka da aka tsugunar a wani yankin mai suna Shabelle. Yanzu haka kungiyar mai gwagwarmaya da makamai ta ce, ta karbe ikon sansanin bayan artabun da ya biyo bayan gumurzun a tsakanin mayakanta dana rundunar AU da aka tsugunar a kasar don wanzar da zaman lafiya.

Wani ganau ya sheda wa kamfanin labarai na Reuters yadda karar fashewar bama-baman na safiyar wannan Talatar, suka tashi jama'a daga bacci tare da haifar da rudani. Al-Shabab dai ta shahara a kai hare-hare a sassan Mogadishu babban birnin kasar don nuna adawa da gwamnatin Somaliya dama sojojin wasu kasashen ketare da ke kokarin taimaka ma gwamnatin.