Al-Shabab sun kashe mutane a Somaliya | Labarai | DW | 26.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabab sun kashe mutane a Somaliya

Mutane 14 sun mutu a Somaliya bayan da kungiyar al-Shabaab ta kai hari kan sansanin sojojin wanzar da zaman lafiya na AU dake kusa da birnin Mogadishu.

Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiyar ta Afirka Kanal Ali Aden Haamud ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na DPA cewa baki dayan maharan kungiyar ta al-Shabaab su takwas da suka kai farmakin sun sheka barzahu. Ya kara da cewa wasu daga cikinsu sun bakunci lahira ne sakamakon tarwatsa abubuwa masu fashewa dake jikinsu da suka yi yayin da wasu kuma suka mutu a yayin bata kashi da dakarun na AU.

A cewar Kanal Haamud dakarun na AU biyar ne suka rasa rayukansu. Sai dai kakakin kungiyar ta al-.Shabaab Sheikh Mohamud Rage ya shaida wa wani gidan rediyo dake goyon bayansu a Somaliya mai suna Andalus cewa sun kashe sojoji 17.