Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya | Labarai | DW | 22.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabaab ta kai hari a Somaliya

Wani dan kunar bakin wake ya kutsa da mota makare da bama-bamai cikin wani gidan cin abinci a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya tare da hallaka mutane da dama.

Harin ta'addanci a Mogadishu

Harin ta'addanci a Mogadishu

Shaidun gani da ido sun tabbar da cewa daga bisani wasu 'yan bindiga sun bude wuta tare da yin harbin kan mai uwa da wabi da kuma yin garkuwa da baki dayan mutanen da ke gidan cin abincin. Wannan hari dai shi ne mafi muni da kasar ta fuskanta cikin wannan shekara. Wani jami'in dan sandan birnin na Mogadishu Mohamed Abdirahman da ya tabbatar da harin ya shaidar da cewa akalla mutane 20 ne suka hallaka ciki kuwa har da mata da kananan yara a abin da ya bayyana da rashin imani. Rundunar 'yan sandan kasar dai ta ce ce tuni aka kawo karshen garkuwa da mutanen da 'yan bindigar suka yi. Tuni dai kungiyar al-Shabaab ta masu kaifin kishin addini da ta addabi kasar ta Somaliya tsahon shekaru ta dauki alhakin harin.